News as Facts

Wani jirgin ‘yan sama jannati ya samu nasarar buge daya daga cikin miliyoyin duwatsun da suke tsala gudu a sararin samaniya

926

Jirgin ‘yan sama Jannatin da hukumar NASA ta harba a ranar litinin mai suna DART ya samu nasarar buge daya daga cikin miliyoyin duwatsun da suke tsala gudu a sararin samaniya. Nasarar dai ta zama wani gwaji mai cike da tarihi da ke nuna karfin dan Adam na dakile barazanar halittun da ka iya ruguza rayuwa a doron kasa.

Tasirin sauyawa dutsen na Asteroid alkibla daga falakin da yake tafiya akai, ya faru ne da misalin karfe 7:14 na yammacin yau a agogon Gabas, watanni 10 bayan da kumbon da NASA ta harba ya tashi daga California don gudanar da gwajinsa na farko.

Lori Glaze, daraktan sashin binciken kimiyar duniyoyin dake sararin samaniya ya ce an shiga wani sabon zamani da dan adam ke da damar kare kansa halittu irinsu duwatsun asteroid mai hatsarin gaske.

Jirgin ‘yan sama jannatin na DART na NASA yayi taho mu gama da dutsen na Asteroid Dimorphos mai tsawon mita 160 mai kama da dalar Pyramid na Masar ne cikin tsala gudun kiomita dubu 14 da 500 cikin sa’a daya, karon da ya sauyawa makeken dutsen alkibla.

Bincike dai ya nuna cewar duwatsun asteroids bas a zama barazana ga duniyar da muke, domin kuwa falakin da suke tsala gudu akansa na da nisan kilomita miliyan 11 da 265 da 408 da duniyar mu.

Sai dai duk da hakan hukumar NASA ta dauki gwajin karkatar da duwatsun na Asteroids da mahimmanci, saboda gaba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.