News as Facts

Wani matashi dan soyayya Ya datse hannun wanda ya zagi budurwarsa

1,162

Wani  matashi dan soyayya Ya datse hannun wanda ya zagar masa budurwa.

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Nasarawa sun kama wani matashi mai shekaru 21 bisa zarginsa da laifin datse hannun wani saboda zagar masa budurwa.

Kakakin rundunar a jihar, DSP Ramhan Nansel ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne ranar Juma’a a ƙaramar hukumar Karu, inda ya yi amfani da adda ya datse hannun matashin.

Hakazalika ya ce, an kamo shi ne ranar Asabar, kuma ya amsa laifinsa.

Sai dai wanda ake zargin ya ce ya yi hakan ne bayan matashin ya zagi masoyiyarsa.

Danladi ya kuma ce, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adesina Soyemi ya ba da umarnin mai da lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar, domin ci gaba da bincike.

Ya kuma ce da zarar an kammala za a maka shi a gaban kotu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.