News as Facts

Yadda wani ya sace wayar dan sanda a caji ofis lokacin da ya je neman beli

262

Ya ‘Sace’ Wayar Dan Sanda A Caji Ofis Lokacin Da Ya Je Neman Beli

Can a jihar legas Mutane sun cika da mamaki lokacin da aka gurfanar da wani mutum, gaban kotu bisa zarginsa da satar wayar dan sanda lokacin da yaje neman beli.

An dai gurfanar da shi ne a gaban kotun Majistare da ke Ogba a jihar Legas ranar Juma’a.

’Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wanda ake zargin ya je caji ofis dinsu da ke Bolade, domin yin belin abokinsa da aka tsare.

Dan sanda mai gabatar da kara, Rachael Williams, ya ce wanda ake zargin ya shiga ofishin ne lokacin da wayar ke ajiye a kan tebur wacce kudin ta ya kai darajar Naira dubu 120.

Kodayake ya musanta zargin satar wayar, amma ’yan sanda duk da haka sun gurfanar da shi kan zarge-zargen sata da shiga ofishin ba bisa ka’ida ba.

A cewar Rachael, gano satar wayar ya jefa ’yan sandan da ke bakin aiki cikin rudani, inda nan take Baturen ’Yan Sandan ofishin ya ba da umarnin gudanar da bincike.

Alkalin kotun, Mai Shari’a O.O. Akingbesote, ya bayar da wanda ake zargin beli a kan Naira dubu 100 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.

Daga nan ne alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar tare da ba da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Kirikiri.

Leave A Reply

Your email address will not be published.